Babu laifi a rinƙa zuwa da yara Masallaci, Yana ma da kyau a rinƙa zuwa dasu ɗin musamman in suka fara girma ta yadda bazasu je sunayin kuka a masallacin ba.
Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya kasance yana ɗaukar Umamah jikarsa a lokacin da yake sallah. Wannan yake nuna halaccin zuwa da yara Masallaci. Hakanan kuma Annabi yaji kukan yaro a Masallaci kuma baiyi hani akan kawo shi ba. Wannan yake ƙara nuni da cewa yana da kyau kuma ba Haramun bane zuwa da yara Masallaci, amma ya kamata duk wanda yaje da yaronsa masallaci ya zamto yana kusa dashi domin kula dashi, sannan kuma kada yaron ya zamto ƙarami sosai ta yadda zaizo yayi ta kuka ko kuma yazo yayi fitsari ko bayan gari acikin Masallacin, sannan kuma kada yaran suyi yawa a Masallacin ta yadda kuma zaa kasa kula dasu,
Leave a Reply