Bismillahirrahmanirrahim.
Ruwa ya rabu kashi uku gasu kamar haka:
•Ruwa mai tsarƙi mai tsarƙaƙewa: Shine ruwa wanda yake a asalinsa, wanda bai cakuɗu da wani abu ba, najasa ko ba najasa ba. Kamar ruwan Kogi, Rijiya, Sama, kududdifi da makamantansu. Duka irin wa’innan ruwa masu tsarƙi ne, ana iya shansu, sannan kuma ana iya yin aikin Ibada dasu.
•Ruwa mai tsarƙi wanda baya tsarƙaƙewa: Shine ruwa wanda ya cakuɗu da abu mai tsarƙi. Kamar ruwan da ya cakuɗu da Siga, ko gari. To wannan ruwa Mai Tsarki ne a karan kansa amma kuma baya tsarkake wa, ma’ana za’a iya shan ruwan, ko kuma ayi aikin gida dashi, amma baza’ayi aiki na ibada dashi ba, kamar alwala ko wankan janaba da makamantansu.
•Ruwa mai Najasa: Shine ruwa wanda ya cakuɗu da najasa ta yadda Sifofin sa suka canza, ɗanɗano, ko wari, ko launi. idan ruwa ya cakuɗu da najasa har wa’innan abubuwa uku ko ɗaya daga ciki suka canza toh baya halatta ayi amfani da wannan ruwa, ko a Ibada ko a aikin gida.
Mas’aloli:
- Idan najasa ta faɗa cikin ruwa mai yawa kamar ruwan rijiya sai najasa ta faɗa aciki, toh ruwan bazai zamto najasa ba har sai najasar tayi rinjaye kan kalan ruwan, ko ɗanɗanonsa, ko Warinsa.
- Ruwa mai gudu kamar ruwan kogi Mai Tsarki ne, Koda najasa ta faɗa aciki, da zarar najasar ta kau za’a iya amfani dashi.
- Ruwa kaɗan idan najasa ta faɗa aciki ta zamto najasa koda ko Sifofinsa bai canza ba. “Kaman ruwa acikin ƙaramin kofi sai najasa ta faɗa acikinsa”ko
Leave a Reply