ALHERI BAYA FADUWA KASA BANZA(Sheikh Aliyu Said Gamawa)

Danna nan domin shiga karatu Online

ALHERI BAYA FADUWA KASA
BANZA:
Yan uwa duk Wanda ya samu
Daman yiwa wani alheri to ya
hanzarta yayi, ko ka samu Daman
tallafawa dangin ka da sauran
al’umma na kusa Dana nesa duk
ka dage kayi cikin lokaci, domin ba
Wanda zai yiwa wani alheri face
Allah ya sakawa Wanda yayi
alherin da ninkin abinda yayi.
Yawan kyauta da kokarin bada
sadaka ga mabukata na kusa
Dana nesa, da yin aiyukan
taimakawa addini, da himma wajen
Gina al’umma ibadace ta bayin
Allah nagari.
Pls mu nisanci Rowa, mu guji
matsin hannu, mu kyamaci
qanqamo, domin halaye ne na
marasa Imani, kuma siffofi ne na
yan wuta. Suna jawo kaskanci da
zubewar mutumci a cikin kowacce
al’umma ta da, da al’ummar yanzu.
Marowaci na gamuwa da suka ta
rashin kima, da mummunan bakin
jini daga kowa, kuma iyalan sa da
duk masu mu’amala dashi suna
cikin kunci wajen kusaci dashi.
Mafi munin Rowa ka yiwa aikin
addini Rowa, da kin tausayawa
masu hakki Akan ka, da watsi da
masu rauni cikin mabukata. Rowa
na jawo ka zauna cikin kunci,
rashin jituwa da mutane, Rowa na
sanya ka gadarwa zuriyarka rashin
alheri da kwadayin Kayan wassu.
Kullum ka rayu cikin buri, ganin
Kai, Jin kyashi da hassada ga
mutane.
Madallah da bawa Mai yawan
alheri ga kowa, kullum yana cikin
farin ciki da nishadi, ga fara’a da
farin jini, mala’ikun Allah na yi
masa fatan alheri a kullum, iyalan
sa na cikin Jin dadin rayuwa kusa
dashi, musulumci da musulmi na
amfana da baiwar da Allah yayi
masa, kuma zai gadar da wannan
dabi’a ta karimci ga zuriyar sa. Zai
samu daukaka da daraja a
rayuwar sa, kuma ga lada a wajen
Allah. Mu sani Wanda ya Baka shi
yace kaima kana kokarin baiwa na
kasa da Kai.
Ana son yawan alherin ne ta
hanyar da sharia ta halatta, wato
ba riya, ba gasa, ba gori, kuma ba
da niyyar biyan bashin wani alherin
ba.
Hakika Allah baya Hana Mai
bayarwa, kuma yawan miqawa
baya jawo talauci, Mai bayarwa
shine madaukaki sama da Mai
karba. sannan tabbas alheri baya
FADUWA kasa banza.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

One response to “ALHERI BAYA FADUWA KASA BANZA(Sheikh Aliyu Said Gamawa)”
  1. Rafi'at sani Avatar
    Rafi’at sani

    Madallah da wannan tunatarwa Allah yasaka ma mlm da alkhairinsa

Leave a Reply

Categories
Latest updates