DOGARO GA ALLAH SAI MAI
IMANI
Hakika yarda da qaddara mai kyau
ko maras kyau alamace ta cikar
imani ga musulmi. Mu sani ya
bayin Allah dukkan abinda Allah ya
hukunta ga bawa tilas sai ya
sameshi, don haka mu daina
matsawa da tilastawa kan mu
samun nasara cikin dukkan abin
muke yi a ko yaushe. Hakika Allah
baya kuskure, kuma sarrafawa, da
wanzuwar komi naga yadda Allah
yaso.
Duk lokacin da kwadayi ko kaunar
wani abu ya rufe mana ido to mu
roka a wajen Allah kuma mu
dogara ga Allah wajen yarda da
sakamakon samu ko rashi. Duk
duniya in da za’a taru mutane da
aljanu to basa iya amfanarwa ko
cutarwa sai da yardar Allah.
Hakika duk wanda ya dogara ga
Allah to Allah zai isar masa. Mi ke
jawo rashin tawakkali, har ana
hasarar imani, da rashin yaqini na
dogaro ga Allah yayin neman wani
abu a rayuwa?
Masu niyyara aure, da ‘yan
kasuwa, da masu takara ta siyasa
ko neman duk wani shugabanci,
da masu niyyar fara wani quduri na
alheri dole duk mu mayar da komi
ga Allah, mu nemi biyan bukata a
wajen SA shi kadai, mu nisanci
nema daga wajen wanin Allah, ko
dogaro da gata, dukiya, karfi,
dabara ko jarunta. Shiri da tsarawa
duk na mutum ne amma tabbas
amincewa da tabbatuwar komi sai
Allah ubangijin talikai.
Mayar da komi ga Allah yana
sanya natsuwa da kwanciyar
Hankali, da kawar da gaba, ko
adawa ta zargi da yawan fada da
juna. Zafin nema baya kawo samu,
kuma wayo da dabara ko yaudara
basa zama sanadi sai da
amincewar Allah.
Allah shine mamallakin komi da
kowa, kuma abinda ya bayar nasa
ne, abinda ya hanama nasa ne,
abinda ya bayar ya karbema duk
nasa ne.
Pls ‘yan uwa mu natsu mu koma
ga Allah wajen nema, addu’a,
rantsuwa, dogaro, kwadayi da
tsammani. Yalwa da falalar Allah
tana da yawa, kowa Allah yaso zai
bashi daga ni’imar sa, ko a
jarrabeshi gwargwadon imanin sa.
Wanda raunin imani da rashin
karfin zuciya na tawakkali ya
figitashi to zai iya kaiwa kansa ga
halaka na hasarar imani, ko ya
zamo mai hassada da baiwar da
Allah yayiwa wani, ko ya fada
tarkon shaidanun bokaye,
masihirta da ‘yan damfara. Pls
kada ka dorawa kowa laifi in ka
rasa, kuma kada kayi alfahari in ka
samu. Abinda ka rasa tabbas
dama ba rabonka bane, abinda ka
samu hakika dama kai aka
qaddarawa shi.
Allah ya kara mana imani, hakuri,
tawakkali, juriya da tsayar da
bukatu, ko rashi ga Allah shi kadai
mabuwayi mai hikima.
Leave a Reply