Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace wanda ya faɗe shi da rana yana mai Imani da shi, mai yaƙini, kuma ya mutu kafin yakai yammaci to yana daga cikin ƴan Aljannah.
Haka nan wanda ya faɗe shi da dare yana mai yaƙini da shi kuma ya mutu kafin ya wayi gari toh yana daga cikin ƴan Aljannah.
Wannan hadisi Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 6306
Wannan Sigar Istigfari nada matuƙar falala da bai dace Musulmi ya barshi ba, sannan kuma domin samun wannan falala dole sai mutum ya samu cikakkiyar Imani da abinda wannan Istigfarin ya ƙunsa yana mai yaƙini dashi, kamar yadda hadisin yayi bayani.
Sigar Istigfarin:
اللَّهُمَّ أنْتَ رَبِّي لا إلَهَ إلَّا أنْتَ، خَلَقْتَنِي وأنا عَبْدُكَ، وأنا علَى عَهْدِكَ ووَعْدِكَ ما اسْتَطَعْتُ، أعُوذُ بكَ مِن شَرِّ ما صَنَعْتُ، أبُوءُ لكَ بنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وأَبُوءُ لكَ بذَنْبِي فاغْفِرْ لِي، فإنَّه لا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إلَّا أنْتَ
Allahumma anta Rabbi la ilaha illa anta, Khalaqtani wa ana ‘Abduka, wa ana ‘ala ‘ahdika wa wa‘dika mastata‘tu, a‘udhu bika min sharri ma sana‘tu, abu-u laka bini‘matika ‘alaiya, wa abu-u laka bidhanbi faghfirli, fa-innahu la yaghfirudhunuba illa anta
Leave a Reply