Fatawoyin Rahama by Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo 18th September 2022

Tambayoyi da Amsoshi:

 1. Mai Injin Niƙa zai iya kuɓuta daga laifin ƙara da Injin yake in yana rage farashin kuɗin niƙa ga Makwabta?
 2. Ma’aikacin Haraji zai iya amfani da wani kuɗi da ake tarawa na Haraji don gudanar da aikinsa ?
 3. Mace in ta yi rantsuwa ba za ta koma gidan Mijinta ta ba sai daga baya ta koma- za ta yi Azumin Kaffara?
 4. Ya hallata Mamu ya yi Jalsatul Istirah a bayan Limamin da baya yi?
 5. Wace Sallah ce Salatul Awwabeen!
 6. Gaskiya ne wanda ya mutu a gona yayi Shahada?
 7. Mai sayar da Zoben zinare zai sayar wa namiji?
 8. Ya ya hallacin aiki a companin dake sai da giya ga wanda yake aiki a ɓangaren da bai shafi giyar ba!
 9. Ya hallata ɗa ya karɓi kuɗi na buƙata a wajen mahaifinsa da yake sana’ar kiɗa da waƙa!
 10. Ya Halaccin albashin wanda ba ya zuwa aiki akan lokacin da aka yi alƙawari da shi saboda ya ce ‘ in shaa Allah’ lokacin da ake yarjejeniyar aiki!
 11. Ya hallata mutum ya ajiye azumi saboda wasu ayyuka da ake buƙata ya yi?
 12. Ya hallata mutum ya karɓi bashin Banki don ya ciyar da Iyalansa?
 13. Menene hukuncin mace mai ciki ta je tayi ‘scanning’ don sanin namiji ko mace za ta haifa!
 14. Adadin ayoyi nawa mai haila za ta karanta?
 15. Ya ya hukuncin masu yin passport din wasu ƙasa don samun Visa shiga wasu ƙasashe cikin sauƙi!
 16. Ɗaurin aure za a fara yi ko Jana’iza idan biyun sun hadu a lokaci ɗaya duba da faɗin Allah ” Kuma lalle Shi ne Ya sa a yi dariya, kuma Ya sa a yi kuka” Suratun Najmi: 43
 17. Menene hukuncin mutum yayi bacci da janaba!
 18. Gaskiya ne duk abin da aka fara ranar Laraba zai yi albarka?
 19. Yaya hukuncin hujin kunne da hanci da mata suke yi?
 20. Mace da ta tuƙa tuwo ya zubo har ya kashe ‘yarta za ta yi kaffara?
 21. Ya hallata mutum ya ɓoye abinci ya zo ya sayar da tsada?
 22. Ana iya mafarkin ganin Allah?
 23. Yaya hukuncin wanda baya bin wata Mazhaba?
 24. Hukuncin wanda aka ba shi kuɗi ya ɗauko babur a Mota sai ya hau Babur din ya taho da shi maimakon ya dora a mota

Download

Click Here to Support our work

Leave a Reply

%d bloggers like this: