HUKUNCE-HUKUNCEN AIKIN HAJJI DA UMRA Darasi na 9(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Danna nan domin shiga karatu Online

SA‘AYI TSAKANIN SAFA DA
MARWA
Bayan kammala dawafi da yin
sallah raka‘a biyu a Makama
Ibrahim, wanda muka yi bayaninsu
a baya, abu na gaba shine sa‘ayi
tsakanin Safa da Marwa.
Safa da Marwa duwatsu ne guda
biyu wadanda ke da tazara a
tsakaninsu, a yanzu an yi bene
sakamakon yawan mutane domin
saukaka cunkoso, bangaren tafiya
daban bangaren dawowa daban.
Akwai kwari a tsakaninsu wanda a
yanzu an yi dirkoki masu koren
fenti, da kwayayen lantarki koraye
wadanda suke nuna farkon kwarin
da kuma karshensa.
SIFFAR SA‘AYI DA SUNNONIN
SA
Ana fara sa‘ayi ne daga Safa, idan
an je Marwa anyi shaudi 1 kenan,
idan an dawo Safa an yi shaudi 2
ke nan.
Haka mai aikin hajji ko umra zai yi
har sai ya yi shaudi 7.
-Idan ka nufi Safa sai ka karanta
wannan ayar:
ﺇﻥ ﺍﻟﺼﻔﺎ ﻭﺍﻟﻤﺮﻭﺓ ﻣﻦ ﺷﻌﺎﺋﺮ ﺍﻟﻠﻪ……. ﺍ
Zuwa karshenta,
sannan ka ce:
ﺃﺑﺪﺃ ﺑﻤﺎ ﺑﺪﺃ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻪ
-Sannan sai ka hau Safa, sai ka
fuskanto Al-kibla sannan ka ce:
ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ, ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ, ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ, ﻻﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ
ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ, ﻟﻪ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﻭﻟﻪ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻳﺤﻴﻲ ﻭﻳﻤﻴﺖ
ﻭﻫﻮ ﻋﻠﻰ ﻛﻞ ﺷﻲﺀ ﻗﺪﻳﺮ, ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ, ﺃﻧﺠﺰ
ﻭﻋﺪﻩ ,ﻭﻧﺼﺮ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﻫﺰﻡ ﺍﻷﺣﺰﺍﺏ ﻭﺣﺪﻩ
-Sannan sai ka roki abin da ka so.
Ana so duk addu‘a da zikiri a
maimaita su sau 3.
-Sannan sai ka tafi zuwa Marwa,
ana so a yawaita zikiri da addu‘oi a
lokacin da ake sa‘ayi.
-A duk sanda ka tarar da koriyar
dirka ta farko da korayen
kwayayen wuta sai ka fara
sassarfa har sai ka je alama ta
biyu sannan ka koma tafiya da irin
tafiyarka (wannan ya shafi maza
ne kawai).
-Idan ka hau Marwa, sai ka aikata
irin abinda ka aikata a kan Safa na
fuskantar alkibla da zikiri da
addu‘oi.
-Daga haka sai ka gangara ka
koma Safa, sai ka aikata abin da
ka aikata a hanyar tahowa na
sassarfa a tsakanin korran
alamomi.
-Idan ka kammala shaudi 7 sai ka
tafi kayi aski ko saisaye. Ita kuma
mace sai ta kama karshen
gashinta, gwargwadon tsawon
gabar dan yatsa, sai ta yanke.
Idan ka yi haka ka kammala
umra.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates