Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wa barakaatuh.
Ƴan uwa Musulmi mu sani yaranmu Amana ne a wuyar mu dole mu kula da Tarbiyyar su. Idan bamu kula dashi ba mu sani Allah zai kama mu akai
Da yawa daga cikin iyaye su kan bar yaransu suna kallace kallace wa’inda basu dace ba musamman Cartoons. Da Hujjar cewa ai cartoon ne babu komai aciki. To mu sani cewa Cartoons da yawa da ake nuna wa yara a wannan lokaci yana ƙunshe da abubuwa munana aciki, na koyar da luwaɗi da Maɗigo da wasu munanan ɗabi’u.
Ka samu lokaci ka zauna a matsayin ka na uba ka lura da abinda yaran ka suke kallo. Haka nan kema ki samu lokaci ki zauna ki lura da abinda yaran ki suke kallo. In kuma ba haka ba zakuyi ta aikin banza kuna gina tarbiyyar yaranku Masu cartoon suna rusa shi.
Akwai tashoshi na Cartoon na Musulunci da yara zasu iya kallo. Ko tashoshi na wa’azuzzuka ko na koyon girki ko na koyon wani abu mai amfani shi ya dace mu rinƙa kama wa yaran mu suna kallo sai su tashi da hazaƙa. Amma irin wa’innan Cartoons da suke kallo babu abinda zai ƙara musu sai lalacewa da kasala da sakalci.
Iyaye kuyi bincike kan wannan Bayani zaku sha mamaki. Allah ya tsare mu. Yasa mu dace.
Leave a Reply