TAMBAYA:
Duk da cewa akwai ayoyi da hadisai da dama da suke kwadaitar da yin aure, amma wani lokacin mutum ba shi da ikon yinsa, ko kuma ka ga mace ta rasa miji shekara da shekaru. Shin wanda ya sami kansa a irin wannan hali zai iya amfani da wasu hanyoyi don biyawa kansa bukata saboda kada ya fada cikin haram?
AMSA:
Wanda ya sami kansa a irin wannan hali, zai ci gaba da yin hakuri da rokon Allah da neman arziki daga gare Shi, don samun ikon yin aure, sannan ya yawaita yin azumi, wanda shi ne yake datse kowace irin sha`awa. Dalili kuwa fadinsa subhanahu wa ta’ala cewa:
وَلْيَسْتَعْفِفِ الَّذِينَ لَا يَجِدُونَ نِكَاحًا حَتَّى يُغْنِيَهُمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِهِ …النور: 33
Ma’ana:
Kuma wadanda ba su sami ikon yin aure ba, su kame kansu har sai Allah Ya arzuta su daga falalarSa…
A nan Ubangiji subhanahu wa ta’ala yana umartar mu da kame kai har zuwa lokacin da ya arzurta mu da falalarsa. Sannan kuma hadisin da ya gabata wanda a cikinsa Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce:
…وَمَنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَعَلَيْهِ بِالصَّوْمِ فَإِنَّهُ لَهُ وِجَاءٌ.
Ma’ana:
…Wanda bai sami ikon yin aure ba, ya yawaita yin azumi, saboda yawaita azumi, yana datse sha`awa.
A nan za mu fahimci cewa, azumi shi ne babban abin da zai taimakawa mutum wajen kame kai daga sha`awa da kuma kara lafiya. Amma yin amfani da wasu hanyoyi wurin fitar da maniyyi, yana cutar da lafiyar mutum, ya kuma jawo rashin kwanciyar hankali, kamar yadda wadansu likitoci suka bayyana. Allah ya sa mu dace, amin.
Leave a Reply