Bayan ɓarkewar wannan annoba ta Covid19 da ta addabi duniya, wasu Ƴan damfara suna amfani da wannan dama domin baje ƙolinsu, ta yadda suke yin amfani da wannan dama wurin sace kuɗaɗen mutane, ya kamata Musulmi ya lura matuƙa kada ya faɗa tarkon irin wa’innan ɓarayin.
Wa’innan ƴan damfara suna da salo daban daban da suke bi wurin yaudarar mutane har mutanen su basu bayanan da suke buƙata wanda kuma sukanyi amfani da wa’innan bayanan wurin satan kuɗin mutane a banki, ko kuma hacking musu facebook account ko Whatsapp account, sai suyi amfani da wa’innan account ɗin wurin tuntuɓar abokan wa’inda sukayi hacking account nashin domin neman kuɗi daga garesu ko kuma domin jefasu zuwa ga wani hatsari.
Da yawa cikin wannan kwanaki mutane sun shiga irin wannan matsaloli. Sabida haka ya dace mu kula sosai mubi matakan kariya da ta dace domin kada mu faɗa wannan tarko.
yana daga cikin abinda ya dace muyi domin kare kanmu:
- Kada ka buɗe wani link da ake turo maka ta whatsapp/Facebook wanda ke nuni da cewa za’a baka kuɗi ko kuma katin waya ko kuma data da makamantansu, duk irin wa’innan link ɗin ba na gaskiya bane kuma zasuyi amfani ne da wannan hanya domin cutarka. Abinda ya dace kayi shine kada ka buɗe irin wa’innan link ɗin, kuma kayi ƙoƙari ka reporting na wannan link ɗin.
- Kada ka yadda ka saka wani bayani da ya shafi asusun ajiyanka a ko wani irin shafi ne har sai ka tabbatar da shafin ingatacce ne.
- Kada ka yadda wani ya kiraka ta waya ya nemi ka bashi Bayananka. Ko na banki ko kuma wanda ya shafeka, ko kuma a turo maka wani code ya kiraka yace maka ka faɗa mishi. Kada ka yarda, domin da haka sukeyi suna sace kuɗaɗen mutane.
Wa’innan kaɗan ne daga hanyoyin da mutum zaibi ya kare kansa.
Abu mafi mahimmanci shine mutum ya zamto mai kula sosai, ko meye ka gani ka bincika sosai kafin ka Amince dashi, sannan kuma mu guje wa yawan son banza, domin da yawa mutane suna faɗawa ne cikin wannan tarko sabida son banza da ganin cewa zasu sami wani kyauta.
Allah yasa mudace, ya kuma daɗa karemu.
Leave a Reply