Musulman Arewa mu farka daga bacci

Danna nan domin shiga karatu Online

Acikin kwanakinnan wasu abubuwa da suka janyo hankalin al’ummar musulmai musamman ƴan Arewacin Nigeria sune:

  • Batun sace yara daga kano zuwa ƙasar iyamurai, da kuma canza musu addini zuwa kiristanci
  • Wasu faifayin bidiyo da sukayi ta yawo a kafafen sada zumunta na yadda kiristoci suke yaɗa addininsu acikin al’ummar Hausawa, da kuma bidiyo da yake nuna yadda wani pastor yake baiwa wasu mata musulmai taimako acikin cocinsa.

Wa’innan abu biyu suna daga cikin abubuwa da suka yaɗu matuƙa a kafafen sada zumunci, sannan kuma anyi ta muhawara kansu, wasu suna nuna baƙin cikinsu, wasu kuma suna ta bayanin yadda za’a samo mafita.

Toh nima ba’a barni a baya ba, zan tofa albarkacin baki na kan wannan batu, a matsayina na Musulmi ɗan Arewa kuma mai kishin Addininsa da Al’ummar sa.

Haƙiƙa sakaci irin namu da nuna halin ko in kula suna daga cikin manyan sabbuba na wa’innan abubuwa da suka auku, ta yadda muna rayuwa ne kara zube, kowa bai damu da kowa ba, ta yadda zaka sami maƙoci bai damu da halin da maƙocinsa ke ciki ba. Haka nan kuma ɗan’uwa bai damu da halin da ɗan’uwan sa ke ciki ba. Uba ya watsar da ɗansa da matarsa, bai damu da cinsu da shansu ko kula da kiwon lafiyansu ba, an haifi yara an barsu kan titina suna garauniya sai kace dabbobi, mutane sun mance cewa wannan yara da Allah ya basu amana ne, kuma zai tambaye su kan wannan amana.

A lokacin da Allah ya baka yaro kaki kula dashi ya tashi ya tambaɗe ya fitini Al’ummah toh kada ka ɗauka baka da laifi, haƙiƙa kana da babban laifi kuma haka za’a cigaba da rubuta maka wannan laifi, domin haƙƙi ne Allah ya baka, kayi watsi dashi.

Abinda nakeso nace shine: da farko rashin kula da ƴaƴa da ake samun wasu iyaye a arewacin najeriya sukeyi ya taimaka matuƙa wurin bada daman sace wannan yara har a wuce dasu zuwa kudu aje a sauya musu Addini.

Sannan kuma sai laifin jami’an tsaro musamman Musulmi daga cikinsu, ta yadda zaka ga motoci suna wuce wa kan titi suna tafiya mai dogon zango amma basu damu da su binciki wa’innan motocin ba domin sanin me suke ɗauke dasu, kuma dama domin haka aka ajiye su akan wannan tituna, da zarar direba yazo ya basu na goro shikenan sai su buɗe masa hanya ya wuce da duk abinda yake ɗauke dashi, koda ko wannan abu zaiyi babban ta’adi wa Al’ummarsu. Su babu ruwansu.

Abinda jami’in tsaro Musulmi ya kamata ya sani shine, Allah zai tambaye shi kan wannan aiki da yakeyi, sannan a lokacin da yake wannan aiki ya kamata a sameshi da kishin al’ummarsa ta yadda zai rinƙa saka ido domin daƙile duk wani abinda zai cutar dasu. Yana yin haka yana neman lada a wurin Allah.

Sannan sai su mutanen Gari da anguwa dole sai mun haɗu baki ɗaya domin taimakon juna, a lokacin da Allah ya mana buɗi muka ga wani yaro yana garauniya a gari iyayensa basu kula dashi toh in muna da hali ya wajaba a kanmu mu taimaka wa wannan yaro don nema masa mafita daga halin da yake ciki, domin in muka barshi ya lalace ƙarshe mu zaizo ya rinƙa cutarwa.

Sai batun yadda kiristoci suke yaɗa addininsu acikin al’ummar mu na hausawa kamar yadda da yawa daga cikinmu munga bidiyon. Wannan abu ne mai matuƙar ƙona zuciya, ace haryanzu ana samun irin wa’innan abubuwa suna aukuwa acikin mu. Toh haƙiƙa ba abinda zamu tsaya muna nuna ɓacin rai da surutai akai bane kawai, dole sai mun tashi munyi abinda ya dace, na wurin kiran mutane zuwa ga wannan Addini na Musulunci, sannan kuma muyi ƙoƙarin karantar da wa’inda suke ciki domin su masa fahimta mai kyau. Ba dole sai kai da kanka ka zama mai da’awah ba, akwai ƙungiyoyi kamar yadda aka sani a wurare da dama acikin arewacin najeriya wadda suke ƙoƙarin kiran mutane zuwa ga wannan Addini, kamar ƙungiyar Wa’azin maguzawa a Kano. Toh irin wa’innan ƙungiyoyi ya kamata a taimaka wa, suci gaba da wannan aiki da sukeyi, domin kare mana al’ummar mu daga halaka. Sannan kuma dole wanda Allah yayi musu wada ta acikin mu su taimaka wa wa’inda basu dashi, sabida kada wa’innan marasa galihun su baƙaci wani abu daga waninmu. Dole a samu jam’iyyoyi wa’inda zasu riƙa gudanar da wannan aiki domin samun cin nasara. Kamar yadda kowa ya sani ne. Musulmi ɗan’uwan Musulmi ne, kuma musulmai kaman gangan jiki ɗaya ne, duk abinda ya samu ɗaya daga cikinmu dole muji ya dame mu baki ɗaya inhar mun kasance masu imani da gaske. Abin baƙin ciki ne matuƙa ace yau matayen musulmai ne suke zuwa coci domin karɓan taimako. Allah yasa mudace, ya kare mana imaninmu ya kuma fitar da Al’ummar mu daga ƙangi da take ciki.

Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive

Leave a Reply

Categories
Latest updates