Shimfiɗa : Tsokaci akan ayoyin ƙarshen na Suratun Nazia’at
Tambayoyi da Amsoshi tare da Dr.Muhammad Sani Umar R/Lemo OON
- Taɓa kare yana warware alwala?
- Yaya hallacin yin sadaƙa a zagayowar ranar da iyayen mutum suka rasu!
- Mace da aka yi mata rasuwa za ta iya raka waɗanda suka zo ta’aziyya har zuwa ƙofar gida?
- Haƙƙin ɗan’uwa akan ɗan’uwansa!
- Wanda ya kwanta asibiti har tsawon kwanaki goma sha ɗaya bai san in da yake ba – in ya samu sauki zai rama sallolin da bai yi ba a wannan hali?
- Matafiyi zai iya yin azumin nafila in ba wahala a cikin tafiyar ?
- Liman zai iya haɗa salloli ko ba dalili?
- Yaya matar mutum za ta yi masa addua in ya mutu!
- Yaya matar da take takaba za ta tantace ƙidayar kwanaki da za ta yi a takaba!
- Mace da ta ji ciwo aka ƙafar har ya goce kafin ta yi wankan tsarki, za a iya rufe wajen da leda akai ta banɗaki ta yi wanka?
- Mutumin da yake aiki a ‘pharmacy’ ya bada magani ba wanda aka zo nema ba, sanadiyar haka wanda ya yi amfani da maganin ya mutu, mai aki a pharmacy yana da laifi, hakanan wanda ya sa shi aiki da rashin cancantasa shi ma yana da laifi?
- Menene hallacin sana’ar siyar da makamai?
- Matsayin yin addu’a a zuciya!
Leave a Reply