Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.
Kowani na miji akwai abinda yake jan hankalinsa wurin auren mace, mafi shahara daga cikin wa’innan sabuba sune kamar haka:
- Kyawu
- Dukiya
- Dangi
- Addini
Wa’innan abubuwa sune mafi yawan abubu wa da suke jawo hankalin na miji ya auri mace.
Shi yasa Annabi Sallallahu alaihi wasallama ya zaba mana abinda yafi daga cikin wa’innan abubuwa guda hudu, shine addini.
Annabi Sallallahu alaihi wasallama yace
تنكح المرأة لأربع: لمالها، ولحسبها، ولجمالها، ولدينها، فاظفر بذات الدين تربت يداك
Ana auran mace dun abubuwa guda hudu.
Dukiyarta, danginta, kyawunta, addininta. Ka zabi mai addini Ka rabauta.
Bukhari: 5090
Muslim: 1466
Babu laifi mutum ya auri mace kyakkyawa, ko mai dukiya amma ta zamto tana da addini, domin inka auri mara addini Ba zai tsaya akanta ba, har yaranka da zata haifa maka zai shafa.
Hakanan ba wai ana nufin mai addini itace wacce ta haddace Al-Qur’ani ko hadisai ba. A’a abinda ake nufi ta zamto in ance mata Allah yace Annabi yace zata bi koda ko bata da ilimi mai zurfi.
Allah yasa mudace
Leave a Reply