By: Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
Yana daga cikin abin da yake Sunnah a ranar idin Layya kada a ci abinci sai bayan an gama sallar idi tukun an dawo. Sannan shi kuma mai abin layya zai yi buda-bakin ne da hantar layyarsa; saboda dalili kamar haka:-
Imamut Tirmiziy ya ruwaito Hadithi na 546, da Imam Ahmad Hadithi na 22,984, da Imam Ibnu Khuzaimah Hadithi na 1426, da Imamud Daaraqudniy Hadithi na 1715, da Imam Ibnu Hibban Hadithi na 2812, da Imam Haakim Hadithi na 1088, da Imamul Baihaqiy cikin Sunan Hadithi na 6380, da Ma’arifatus Sunan Hadithi na 1912 da Isnadi Sahihi daga Sahabi Buraidah Bin Susaib Allah Ya kara masa yarda ya ce:
((كان النبي صلى الله عليه وسلم لا يخرج يوم الفطر حتى يطعم، ولا يطعم يوم الأضحى حتى يصلي)).
Ma’ana: ((Annabi mai tsira da amincin Allah ya kasance ba ya fita a ranar idin Azumi har sai ya ci abinci tukun, to amma ba ya cin abinci a ranar idin Layya har sai ya yi salla tukun)).
A riwayar Ahmad, da Daaraqudniy, da Baihaqiy Sahabi Buraidah ya ce:-
((ولا يأكل يوم الأضحى حتى يرجع فيأكل من أضحيته)).
Ma’ana: ((Ba ya ci a ranar Layya har sai ya dawo tukun sannan ya ci daga layyarsa)).
A wata riwayar Baihaqiy cikin As-Sunan, da Ma’arifatus Sunan Sahabi Buraidah ya ce:-
((وكان اذا رجع اكل من كبد اضحيته)).
Ma’ana: ((Ya kasance idan ya dawo sai ya ci daga hantar layyarsa)).
**************
KO WANDA BAI DA LAYYA SHI MA ZAI YI WANNAN KAMUN-BAKIN?
Hambaliyyah suna ganin wannan kamun-baki ya kebanci mai layya ne kawai.
Amma Hanafiyyah da Malikiyyah suna ganin al’amari ne da ya shafi kowa da kowa.
Mu abin da ya bayyana gare mu shi ne: Mai yin layya da mara layya duka su kame bakinsu har sai bayan salla; mai layya sai ya buda bakinsa da hantar layyarsa, shi kuwa mara layya sai ya buda bakinsa da abin da ya saukaka; saboda Umumin fadar Allah: ((Hakika kuna da kyakkyawan koyi game da manzon Allah)). Da kuma fadarSa: ((Ku ji tsoron Allah iya iyawarku)). Shi mara layya ya ji tsoron Allah ya yi koyi da Annabi har inda karfinsa ya gaza; watau inda a kai lokacin da aka zo maganar yin buda-baki da hantar layya, sai ya zamanto shi ba yi da layyar, ke nan sai ya yi buda-baki da abin da ya saukaka a gare shi.
Allah ne Muke rokon taimakon Shi har kullum. Ameen.
Leave a Reply