Danna nan domin shiga karatu Online
A wannan darasi za mu amsa tambayoyi kamar haka; *Tambaya: Mene ne sharuddan layya? AMSA: Yana daga cikin sharuddan layya: abin da za a yanka, lallai ya kasance daga cikin “bahimatul anʿām” (dabbobin ni’ima), irin su: rakuma da shanu da awaki da tumaki). Domin haka, ba ya cikin sharuddan layya, a yi ta da namun…
·
A yau za mu amsa wadannan tambayoyi. *Tambaya: Wace dabba ya kamata a yi layya da ita? AMSA: Malamai sun yi sabani akan dabbar da aka fi so a yi layya da ita; Imam Mālik da daya daga cikin riwayar Imam Ahmad suna ganin cewa: rago shi ne yafi, sai shanu sannan sai rakuma. Ibn…
·
Kalmar Ahlussunnah kalma ce da take nufin ma’abota sunnar Annabi (S.A.W), ma’ana wadanda suke kan sunnar Annabi (S.A.W) a cikin akida da ibada da mu’amala. An fara amfani da wannan suna tun a cikin karni na daya, a lokacin da bidi’o’i da fitintinu suka kunno cikin wannan addini kamar yadda babban tabi’in nan Muhammad Bin…
·
Bayan godiya da fadanci mai kyawo mai dadi ga madaukakin sarki, limamin ya yi kira ga musulmi mu ji tsoron Allah, ya tsoratar dangane da duniya da rudinta. Ya karanto ayoyin alkur’ani masu nuna muhimmancin tsoron Allah da kasancewarsa shine babban guzuri ga musulmi. Kasancewr wannan huduba ita ce ta karshe a wannan shekara, limamin…
·
Me Zamu Yi A Ranar Ashura? Ranar Ashura ita ce rana ta goma ga watan Muharram, watan farko a kalandar musulunci kuma daya daga cikin watanni hudu masu alfarma da madaukakin sarki ya fade su a cikin Alkur’ani (Suratut Taubah: 36). Manzon Allah (SAWW) ya bayyana falalar wannan watan da kuma musamman kwana goma na…
·
Hindu A Ranar Uhud Kasancewar mun kira sunan wannan baiwar Allah a cikin zancen ta’addancin da aka yi wa sayyadi Hamza kuma don tabbatar da adalcin da muka yi alkawali tun da farko a cikin wannan rubutu zai dace mu yi nuni da cewa, game da kisan sayyidus shuhada’i; Hamza ya tabbata cewa an yi…
·
Makokin Ashura Juyayi da makokin Husaini babu shakka wata bidi’a ce babba da take da manufar ci gaba da tona mikin da tuni wadanda suka yi shi sun gamu da Allah ya hukunta su. Da yana cikin addini a yi makokin wani ai kuwa da an shar’anta ayi na kakan Husaini wanda shi ne fiyayyen…
·
Mu Koma Kan Yazid Nuni ya gabata a can baya zuwa ga irin sabanin mawallafa a game da Yazid. Bisa ga wannan ne mutane suka kasu kashi uku a kan shi. Wasu na zagi har ma da la’antar sa, wasu na yabon sa da gwarzanta shi. Kashi na uku su ne wadanda suka tsaya a…
·
Matsayin Malaman Sunnah Game Da Tawaye A Kan Sarki Yazid 2. Muhammad Bin Ali Bin Abi Talib A cikin yawon da suka yi na neman goyon bayan jama’a, wadanda suka shirya tawayen a Madina sun je wurin kanen Husaini; Muhammad wanda aka fi sani da Ibnul Hanafiyyah. Muhammad ya tambaye su, mene ne dalilinku na…
·
Matsayin Malaman Madina Game Da Tawaye A Kan Sarki Yazid 1. Ibnu Umar: Kamar yadda muka gani a baya sayyidina Abdullahi dan Umar na cikin wadanda ba su yi na’am da nadin Yazidu ba. Amma da ya ga jama’a sun yi masa mubaya’a a bayan mutuwar babansa sai ya kyamaci ya fita daban daga al’umma.…
·
Matsayin Malaman Sunna Game Da Tawayen Mutanen Madina Game da tawayen mutanen Madina malamai magada Annabawa ba su ja bakinsu ba suka yi shiru lokacin da abin yake faruwa. Sun bayyana ma mutane abinda Allah ya wajabta na da’ar shugaba ko da fasiki ne. Maslahar da ke cikin wannan ita ce, kauce ma abinda zai…
·
Matsayin Malaman Sunna A Kan Wadannan Fitinu Annabinmu Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya sanar da cewa fitinu zasu gudana a bayansa. Kuma ya fadi cewa alherinka yana gwargwadon nisantarka daga gare su. Wadannan hadisai suna nan a shimfide cikin littafan Sunna a Kitabul Fitan na kowane littafi. Duba alal misali: Sahihul Bukhari, Kitabul Fitan,…
·
Halin Da Ake Ciki A Makka Rundunar Husain bn Numair wacce take tsare da Ibnuz Zubair da jama’arsa suna can suna dako a wajen birnin Makka, ba su samu labarin mutuwar sarki Yazidu ba sai bayan sati 3 cur. Abu kadan ya rage wannan runduna ta hada kai da Ibnuz Zubair bayan da suka samu…
·
Mutuwar Sarki Yazid Ga dukkan alamu Yazidu ya bar duniya da juyayin abu guda daya da yake fargaban gamuwa da Allah a kan sa. Wannan lamarin kuwa shine kisan Husaini da danginsa. An fadi cewa, karshen kalaman da ya furta a duniya su ne: “Ya Allah! kada ka rike ni da abinda ban so ba…
·
A Makka tun da labarin Karbala ya je ma su sai Abdullahi bin Zubair ya nemi goyon bayan jama’a a kan zama khalifa. Kuma ya samu nan take. Kamar dai mutanen Makka na ganin duk gwamnatin da ta iya tafka wannan danyen aiki to, tawaye a kan ta ya zama wajibi. A Madina birnin Manzo…
·
Me ya biyo bayan kashe Husaini? Bayan da mutanen Kufa suka ga abinda ya faru a ranar Ashura sai suka hakikance sun ci amanar sayyidina Husaini tun da su suka gayyato shi amma kuma suka tozarta shi. Sun fito da shi daga amintaccen gari kuma sun yi biris da zuwansa har mai aukuwa ta auku.…
·
Husaini (Radhiyallahu Anhu) ba shi kadai Allah ya azurta da shahada ba a Karbala. Akwai da dama daga cikin ‘yan uwansa da ya fito da su wadanda suka hada da kannensa Ja’afar da Abbas da Muhammad da Abubakar da Umar da Usman dukkansu ‘ya’yan sayyidina Ali. Akwai kuma ‘ya’yan wansa Al-Hasan: Abdullahi da Qasim da…
·
Kisan sayyidina Husaini ya yi kama da kisan sayyidina Zubair bin Al Awwam dan gwaggon Manzon Allah Safiyyah bint Abdil Muttalib (R.A) wanda ya kasance tare da su Nana Aisha a cikin yakin basasar rakumi. Yakin da makasan sayyidina Usman; wadanda suka yi masa juyin mulki suka hasa wutarsa tsakanin sarkin musulmi Ali da talakawansa…
·
Labarin Kisan Husaini Ya Game Duniya Da sauri kuma ba da bata lokaci ba wannan mugun labari ya game duniya. Ana mamaki ya aka yi musulmi mai neman ceton Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya iya kashe jikansa, farin cikin rayuwarsa?! Wannan labari ya mantar da musulmi sauran musibu da fitinun da suka…
·
Wa ya kashe sayyidina HUSAINI? Bayan duk bayanin da ya gabata na abinda ya faru, muna son amsa wannan tambaya. WA YA KASHE SAYYIDINA HUSAINI? Amma a wannan karon littafan Shi’ah kadai muke son su bada amsa. 1. Ga abinda Allamah As Sayyid Muhsin Al Amin ya fada a cikin A’yanus Shi’ah (1/34): ﺑﺎﻳﻊ ﺍﻟﺤﺴﻴﻦ…
·