Latest Updates

Danna nan domin shiga karatu Online

  • ME YA FARU A KARBALA? 10(Dr. Mansur Sokoto)

    Nadin Yarima Mai jiran gado Kamar yadda muka fadi a baya, HUSAINI Radiyallahu Anhu ya bi umurnin wansa Al Hasan wajen yin biyayya ga gwamnatin sayyidina Mu’awiyah har sanda Allah ya kawo karshenta a shekara ta 60H. To, amma kafin haka Mu’awiyah ya ayyana Yazid a matsayin Yarima wanda zai gaje shi idan ajalinsa ya…

    ·


  • RANAR SALLAH(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

    Daukakar guri, da Daukakar zamani, ayau dukkan alhazai, suke, gabatar da, aiyuka, guda biyar 1- Jifa, Sun jefi Babbar jamra, da duwatsu bakwai- bakwai, 2- Sunyi aski, ko saisaye, mata sun rage gashin kansu, 3- Sunyi yanka, musamman ga masu, Tamattu’i da Qirani 4- Sunyi Dawafi, musamman ga wadanda suka gaggauta 5- Sunyi Saayi, Su…

    ·


  • KHUDUBAR RANAR ARFA 9-12-1434(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

    Bayan yabo da kirari ga Allah, da salati, da sallama, ga Annabi saw, Malam ya bude da ayar da tayi magana akan Amana da Dan Adam ya dauka, bayan Allah ya bijirar da ita ga sammai da kassai da duwatsu, sunki dauka saboda wahalarta. 1- Magana akan kadaita Allah da bauta. 2- Dacewa da gamaiwar…

    ·


  • JIFAN SHEDAN DA TARIHINSA(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

    1- Ya tabbata a tarihi wanda ya fara jifan shedan shine, Annabi Ibrahim saw, lokacin da Allah taala, ya umarceshi,a mafarki, ya yanka dansa, sunzo bayan gari, a mina shine shedan, ya biyoshi, yana gaya masa cewa wannan mafarki ba gaskiya bane, shine Annabi Ibrahim as, ya jefeshi, da duwatsu bakwai, har sai da kafafunsa…

    ·


  • KWANAN MUZDALIFAH(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

    Malamai sunyi magana uku gamai da kwanan Muzdalifah 1- Wajibine,daga wajibobin hajji wanda ya barshi, sai yayi yanka, maganar mafi yawan malamai 2- Kwanan Muzdalifah rukuni ne daga rukunan hajji, hajji baya cika sai da shi, raayin wasu malamai biyar daga cikin tabi’ai, 3- Kwanan Muzdalifah, Sunnah ne, kawai, inji Mal, Shafi’i amma maganar da…

    ·


  • RUWAN ZAMZAM MAI ALBARKA(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

    Tarihin wannan ruwa, kamar yadda yazo a cikin Sahihul Bukhari, Lokacin da Annabi Ibrahim (AS) ya ajiye matarsa,da dansa, a wajan, Mala’ika Jibrilu, ya buga wajan da duddugansa, sakamakon haka aka sami ruwan Zamzam, Wannan ruwa dashi aka wanke zuciyar Annabi saw, a lokacin yana dan shekara hudu, a wajan Halimatus- Sadiya, da kuma lokacin…

    ·


  • KWANAKIN HAJJI (RANA TA BIYU)(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

    Rana ta biyu itace ranar Arfa, Manzon Allah saw yace, Babu wata rana da Allah yake yanta bayi daga wuta, kamar ranar Arfa, Muslum A wani Hadisin yace: Mafi alkhairin Addu’a itace Addu’ar ranar Arfa, Attirmiziy, Azumin ranar Arfa, yana kankare zunubin shekarar data gabata, da mai zuwa, Muslum, ( wannan ya shafi, wadanada basu…

    ·


  • KWANAKIN HAJJI(Mal.Aminu Ibrahim Dauraw)

    Kwanakin Hajji guda Shida ne, (rana ta daya) 1- Ranar takwas ga wata, Ranar tarwiyyah, abubuwa shidda Alhazai zasuyi 1- Yin wanka, Yanke farce, sa turarai( gamai tamattu’i kawai) 2- Daura Ihrami ga namiji, Gyauto da Mayafi, mace kuwa, duk kayan da babu kwalliya tare dasu 3- Niyyar Hajji, a zuciya, ga mai tamattu’i, (amma…

    ·


  • ALHAJRUL-ASWAD(Mal.Aminu Ibrahim Daurawa)

    Hadisi ya tabbata cewa wannan dutse daga cikin Aljannah yake, kuma lokacin da aka saukar dashi fari ne, kal, yawan sabon mutane yasa ya zama, baki, wannan dutse, yasha gwagwarmaya iri-iri, a tsawon tarihi, lokacin da kuraishawa zasu sabinta ginin kaabah, lokacin Manzon Allah saw, yana da shekara talatin da bakwai, sunyi sabani, gamai da…

    ·


  • ME YA FARU A KARBALA 9(Dr. Mansur Sokoto)

    HUSAINI Radiyallahu Anhu ya Lizimci kawaici game da abinda wansa ya yi na mika ragamar mulki ga sayyidina Mu’awiyah, amma a zuciyarsa bai ji dadi ba kamar yadda akasarin mutanen Iraqi ba haka suka so ba amma dai ya daure ya yi mubaya’a tare da sauran jama’a. Ba wani rahoto da ya nuna ko sau…

    ·


  • ME YA FARU A KARBALA 8(Dr. Mansur Sokoto)

    Matsayin Sayyidina Hussaini game da gwamnatin Yazid Kafin mu je can, yana da kyau muyi waiwaye game da gwamnatin da ta kawo shi mulki, ina nufin gwamnatin babansa Mu’awiyah. Abinda aka sani ne cewa, har zuwa lokacin wafatin sayyidina Ali (R.A) ba wani nadadden sarkin musulmi in ba shi sayyidina Ali din ba. Babu kuma…

    ·


  • ME YA FARU A KARBALA 7(Dr. Mansur Sokoto)

    Kafin mu karkare magana kan Yazidu yana da kyau a san abubuwan da Ahlussunna ke la’akari da su wajen yanke hukunci a kan kowane mutum. 1. Musulmi duk yana da alfarmar da ya kamata a kiyaye masa. Ba ya halasta a shiga rigar mutuncinsa sai da dalili tabbatacce. 2. Kuskure a wajen kyautata ma musulmi…

    ·


  • ME YA FARU A KARBALA 6(Dr. Mansur Sokoto)

    Har yanzu dai a kan Yazid Mun riga mun fadi cewa, akwai rikici mai yawa a tsakanin mawallafa game da sha’anin Yazidu har mun soma bada wasu ‘yan misalai a kan haka. Daga cikin abin da ke nuna haka zamu ga zancen wasiyyar da Mu’awiyah ya yi masa, malam Dinawari da Ibnu Abdi Rabbihi duk…

    ·


  • ME YA FARU A KARBALA 5(Dr. Mansur Sokoto)

    A cikin babban kundin tarihin da Ibnu Asakir ya wallafa ya kawo hadisai masu dinbin yawa a kan zagin Yazid kamar yadda ya al’adanta a duk wadanda yake kawo tarihinsu. Sai ka ga ya kawo ruwayoyi masu yawa a kan yabon mutum, sai kuma ya kawo wasu irin su na sukar sa. Muradin mawallafa a…

    ·


  • ME YA FARU A KARBALA? 4(Dr. Mansur Sokoto)

    Rikicin mawallafa a game da YAZIDU Yana da wahala kwarai ka samu mutum a tarihi wanda aka yi ta takin saka a kansa, ruwayoyi kuma suka rinka cin karo da juna a kan sa kamar YAZIDU. Yawan masoyansa masu yabon sa, da makiyansa masu sukar sa na sanya mai karatun tarihi a cikin rudani ba…

    ·


  • ME YA FARU A KARBALA 3(Dr. Mansur Sokoto)

    Wane ne YAZIDU? Sunansa YAZIDU Dan Mu’awiyah Dan Sakhr (Abu Sufyan) Dan Harb Dan Umayyah Al Umawy Al Qurashie. Ana yi masa alkunya da Baban Khalid. Mahaifiyarsa ita ce Maisun ‘yar Bahdal daga kabilar Kalbu, daya daga cikin kabilun Kuraishawa masu karfi a wancan lokaci. Ta rabu da mahaifinsa tana dauke da cikinsa, sai ta…

    ·


  • ME YA FARU A KARBALA 2(Dr. Mansur Sokoto)

    Assalamu alaikum jama’a. Ina kara jaddada barka da sallah a gare ku gaba daya. Allah ya karbi ibadarmu. Zamu ci gaba da darasi na biyu a yau in sha Allah. Tun da farko zai yi kyau mu soma da takaitaccen tarihin mutane biyu wadanda zancen Karbala yake kewaya a kan su. Su ne: Sayyidina HUSAINI…

    ·


  • HUNDREDS DEAD IN NIGERIA DETENTION, AMNESTY SAYS From: BBC news 14 October 2013

    Most of the dead are thought to be connected to the militant group Boko Haram Hundreds of people have died in detention facilities in north-east Nigeria as the army tries to crush an Islamist militant rebellion there, according to Amnesty International. The human rights group said some detainees died from suffocation in overcrowded cells, others…

    ·


  • THE 10 DAYS OF ZUL HIJJA(Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi)

    The ten days of Zul Hijjah are the first ten days of the 12th Islamic calendar month called Dhul Hijjah. These are the days when most of the pilgrims make a journey to Makkah and perform their tasks of Hajj. Just as they have a special chance to get extra reward, the ones who were…

    ·


  • ME YA FARU A KARBALA?(Dr. Mansur Sokoto)

    GABATARWA: Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai Da yawa daga cikin mutane suna tsammanin malaman Sunnah da suka ce a kame baki daga kutsawa a cikin rikittan da suka faru a tsakanin iyayenmu musulmin farko sun fadi haka ne don suna son a boye gaskiya. Wannan kuwa kuskure ne babba. Tarihin magabata, musamman ma…

    ·


Donate

Bada gudunmawa domin Yada Addinin Musulunci
Account Number: 4568496377
Bank: Moniepoint
Name: Islam Online Archive